Hukumar Raba Tattalin Arziki Ta Ƙaryata Miƙa Wasu Rijiyoyin Ɗanyen Mai Ga Wasu Jihohi

[ad_1]

Hukumar rabar da tattalin arzikin ƙasa, ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka wallafa cewar, an bayar da shawarar, a miƙa wasu Rijiyoyin Ɗanyen Man Fetur ga wasu jihohin, da ke da arzikin Man.

Shugaban Hukumar Dakta Mohammed Bello Shehu, ya ƙaryata rahotannin a cikin sanawar da ya fitar.

Ya ce, ba wani mataki da ɗauka mai kamar haka, kuma rahotannin, ƙarya ne tsagwaransu kuma an wallafa su ne, kawai bisa nufin karkatar da tunanin mutane.

  • Gwamna Dauda Lawal: Tsayayyen Namiji A Siyasar Yankin Arewa Maso Yamma
  • APC Ta Tsawaita Rijistar Mambobinta, Ta Ɗage Ranar Babban Taronta Na Ƙasa

Ya ce, an ankarar da Hukumar kan batun rahotannin na ƙarya cewa, kwamtitin haɗaka a tsakanin Hukumomin gwamnati da ke kan aikin tantance taƙaddamar mallakar Rijiyoyin Ɗanyen Man da kuma na Iskar Gas cewa, an miƙa su ga wasu jihohin, da ke da arzikin Man, batun bah aka bane.

Dakta Shehu ya ƙara da cewa, waɗannan rahotanni ba da yawan Hukumar, aka wallafa sub a ko kuma matsayar da da kwamitin ya cimma ba.

Ya ci gaba da cewa, a wannan matakin da ake a yanzu, cimma ta karƙashe ko kuma wata shawara da aka bayar ta cewa, an miƙa wasu Rijiyoyin Ɗanyen Man Fetur ga wasu jihohin, da ke da arzikin Man, inda ya ce, wannan taƙadamar, batu ne, da a yanzu, ake bin shi daki-daki, ba da garazaje ba.

Shehu ya ƙara da cewa, Hukumar na tabbatar da tana yin takatsantsan da bin ƙa’ida, wajen gudanar da ayyukanta, da suka shafi lamarin ƙasa, musamman batu na taƙaddamar mallakar Ɗanyen Mai da kuma Iskar Gas.

Shugaban ya ce, a ranar 13 ga watan Fabirairun 2026 ne kawai, Hukumar ta karbi wani rahoto daga gun kwamtin na hukumomin gwamnati, bisa ƙa’idojin da ka gindaya.

Ya ƙara da cewa, an miƙa kundin rahoton zuwa ƙwararrun masu ruwa da tsaki, domin yin nazari, a kansa.

A cewarsa, hukumar da za su gudanar da nazarin su ne, Hukumar da ke sanya ido kan Man da ake haƙowa na kan tudu da Hukumar da ke sanya ido kan iyakokin ƙasa da ofishin Sifiyo Janar na ƙasa.

Shehu ya ci gaba da cewa, waɗannan hukumomin za su yi nazari kan kudin rahoton a cikin nutsuwa gaga bisani, su mika rahton ga kwararrun da zasu sanya sanya da kuma shawar da za su baiwa hukumar, domin ta dauki mataki nag aba.

Ya shawarci yan kasar nan, da sauran masu ruwa da tsaki dasu yi watsi da rahoton na kazan kurege da kafafen suka wallafa kan wannan batun amma su jira bayanin da hukumarsa za ta fitar bayan kammala nazarin da ke yi, kan batun.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *