Kamfanin Kasar Sin Ya Ba Da Gudummawar Kwamfutoci Da Magungunan Zazzabin Cizon Sauro A Kudancin Benin
[ad_1]
Wani kamfanin kasar Sin ya bayar da gudummawar kayan aikin fasahar sadarwa (IT) da magungunan yaki da zazzabin cizon sauro ga Asibitin Jami’ar Abomey-Calavi/So-Ava dake kudancin Benin, a jiya Talata.
Gudummawar wadda ta kunshi kwamfutocin tafi-da-gidanka 40 da katan-katan masu yawa na magungunan zazzabin cizon sauro, wani bangare ne na shirin bunkasa kasuwanci mai lakabin “Kamfanoni 100 a cikin kauyuka 1,000”.
Da yake jawabi a bikin mika kayayyakin, jakadan kasar Sin a Benin Zhang Wei ya yaba da hadin gwiwar dake tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasar Benin.
Ya bayyana cewa, ofishin jakadancinsu ya dade yana jajircewa wajen karfafawa da ba da goyon baya ga kamfanonin kasar Sin dake aiki a Benin domin ganin sun sauke nauyin dake wuyansu na kyautata walwalar al’umma.
Da yake karbar gudummawar, magajin garin Abomey-Calavi, Angelo Ahouandjinou, ya mika godiyarsa ga kamfanin na kasar Sin. Yana bai bayyana cewa, “Bisa bayar da wannan gudummawar kayan aiki na fasahar sadarwa, kun sake nuna jajircewarku ga ci gaban yankinmu da kuma halacci wajen kyautata walwalar al’umma.” (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link