Wanzar Da Tsaro Da Daidaito A Yankin Mashigin Hormuz Zai Kare Moriyar Dukkanin Al’ummun Duniya

[ad_1]

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce mashigin teku na Hormuz, da sassan dake yankin na da matukar muhimmanci ga sassan kasa da kasa ta fuskar safarar hajoji da cinikayyar makamashi.

Mao Ning, wadda ta bayyana hakan a Larabar nan yayin taron manema labarai, ta kara da cewa wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin mashigin, mataki ne na kare moriyar bai daya ta sassan kasa da kasa.

Jami’ar ta kara da cewa, kasar Sin na kira ga dukkanin sassa da su dakatar da aiwatar da matakan soji, su kauracewa kara ta’azzara yanayin tashin hankali, kana su aiwatar da matakan kandagarkin rashin daidaito, wanda ka iya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *