Dimokuradiyyar Dake Shafar Kowa a Sin Ingantaccen Karfi Ne Na Ingiza Shirin Raya Ci Gaban Sin Da Zamantakewar Al’umma Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15
[ad_1]
Taron shekara-shekara na NPC da na CPPCC na Sin, muhimmiyar taga ce ta fahimtar yadda ake zamanintar da al’ummar Sinawa, da aiwatar da dimokuradiyya mai shafar kowa da kowa. Ta hanyar wannan muhimmin dandalin, wakilai da ‘yan majalisar bayar da shawara suna gabatar da shawarwari masu kyau, suna sa karin ra’ayoyi daga jama’a su kai ga shugabanni masu yanke shawara kai tsaye, sannan sun zama manyan manufofin kasar, wanda ke nuna karfin dimokuradiyyar irin ta Sin dake shafar kowa da kowa.
Ma’aunin Edelman Trust Barometer da aka buga ya nuna cewa, amincewar jama’ar Sin da gwamnati, da kamfanoni da sauransu ya ci gaba da zama na farko a cikin kasashen da aka yi nazari a kai, kuma kyakkyawan fatansu game da nan gaba ya tsaya a matsayin na farko a duniya. Masana na ganin cewa, nasarar aiwatar da dimokuradiyya irinta kasar Sin, ba wai kawai ya ba da kariya a bangaren tsare-tsare ga aikin zamanintar da jama’a ba, har ma ya samar da misali mai amfani ga yawancin kasashe masu tasowa, don bullo da tsari irin nasu na dimokuradiyya, da ya dace da yanayin kasarsu, ya kuma wadatar da yanayin siyasar bil’adama.
Shirin raya ci gaban Sin da zamantakewar al’ummar na shekaru biyar-biyar karo na 15 ya fara aiki a wannan shekara da muke ciki, kuma Sin ta shiga sabon tafarki na zamanintar da al’umma. Tsarin aiwatar da dimokuradiyyar dake shafar kowa da kowa zai ta kara kuzari a cikin aikin zamanintar da al’umma, kuma zai kawo karin haske da damammaki ga duniya. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link