’Yan bindiga sun harbi wani saboda rashin isassun kuɗi a asusunsa

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da karɓar Naira miliyan biyu a hannun wani mutum, sannan suka harbe shi saboda kuɗin ba su kai adadin da suke nema ba.

Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka mai shekaru 25, Uche Okechukwu, da Somto Chukwuma.

Sun harbi mutumin a ƙafa bayan sun gano ba shi da kuɗi sosai a asusun bankinsa.

Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya ce sun samu kiran gaggawa cewa an yi garkuwa da wani mutum a gidansa da ke Ogwashi-Uku.

’Yan sanda sun bi sahun masu garkuwar har cikin daji a yankin Ogwashi-Uku, inda suka ceto mutumin da da raunin harbin bindiga.

Bincike ya kai ga kama Nka da Okechukwu a Jihar Anambra, inda aka kuma gano motar mutumin da suka harba, ƙirar Toyota Venza.

Bayan amsar laifin da suka yi, ’yan sanda sun kai samame wata mafakarsu da ke ƙauyen Agidiase, Ogwashi-Uku, inda suka kama wanda ake zargi na uku.

Masu garkuwar kuma sun nuna wa ’yan sanda inda suke ɓoye kayan aikinsu, inda aka gano motar da suke amfani da ita da kuma na’urar katse sadarwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *