Dukiyar Elon Musk ta kai dala biliyan 839 — Forbes
[ad_1]
Fitaccen attajirin duniya, Elon Musk, ya zama mutum mafi arziki da aka taɓa samu a tarihi, yayin da dukiyarsa ta kai kimanin dala biliyan 839, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana a sabuwar ƙididdiga ta jerin attajiran duniya da ta fitar.
Rahoton ya ce Musk ne ya sake zama lamba daya karo na biyu a jere a jerin Forbes World’s Billionaires, bayan da dukiyarsa ta ƙaru da kusan dala biliyan 500 cikin watanni 12 da suka gabata.
An ce hauhawar darajar kamfanoninsa na Tesla da SpaceX, wadda ke shirin shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari a 2026, ne suka taimaka wajen ƙaruwar dukiyarsa.
Forbes ta ce Musk shi ne mutum na farko a tarihi da dukiyarsa ta haura dala biliyan 800, kuma yana kan hanya ta zama mutum na farko da dukiyarsa za ta kai dala tiriliyan guda.
Rahoton ya kuma nuna cewa yawan attajirai a duniya ya kai mutum 3,428, yayin da jimillar dukiyarsu ta kai dala tiriliyan 20.1 — mafi girma da aka taɓa samu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link