Matatar Man Fetur Ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Da Dizal
[ad_1]
Matatar Man Fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur da gas (AGO), wanda hakan ke nuna raguwar farashi na farko bayan karuwar farashi da aka samu a ‘yan kwanakin nan.
A cewar sabon rahoton farashin matatar da aka fitar a ranar 10 ga Maris, 2026, an rage farashin mai da N100 inda ya dawo N1,075 a kowace lita, wanda yake a baya akan N1,175 a kowace lita.
Bugu da ƙari, an rage farashin dizal zuwa N1,430 a kowace lita, wanda ke nuna cewa, an samu ragowar N190 daga farashin farko na N1,620 a kowace lita.
[ad_2]
Source link