Amurka ta soke bizar Wole Soyinka
[ad_1]
Fitaccen marubucin nan ɗan Nijeriya wanda ya taɓa lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce gwamnatin Amurka ta soke bizarsa tana mai haramta masa shiga ƙasar.
Farfesa Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Legas a ranar Talatar nan.
Ya bayyana cewa Ofishin Jakadancin Amurka ne ya sanar da shi batun ƙwace bizar a wata wasiƙa da ya aike masa.
Sai dai ya sanar da cewa ba shi da masaniya kan wani mummunan laifi da ya aikata da har zai sa Amurkan ta soke bizar da ta ba shi.
“Ya zama dole ne na kira wannan taron saboda mutanen Amurka da ke tsammanin zuwana wasu taruka da cewa kar su ɓata lokacinsu.
“Ba ni da biza; an haramta min shiga Amurka. Saboda haka idan kuna son ganina, kun san inda za ku same ni,” in ji Soyinka.
“Har yanzu ina bibiyar tarihina na baya… Ba ni da wani tarihin aikata laifuka a baya ko ma babban laifi ko rashin ɗa’a da zai sa in cancanci a soke min biza.
“Na fara waiwayen baya—shin na taɓa yi wa Amurka wani rashin adalci? Shin ina da wani mugun tarihi? An yanke min hukunci? Shin na saɓawa wata doka a ko’ina?”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link