Yadda Mutanen Gari Suka Ƙone Matashi Kan Ƙwace Waya A Kano
[ad_1]
Wasu fusatattun matasa a unguwar Dorayi Ƙarshen Waya a Jihar Kano, suka ƙone wani matashi har lahira kan zargin yunƙurin ƙwace wayar wata mata.
Shaidu sun ce wanda ake zargin ya caka wa matar wuƙa a kirji yayin da suke kokawa, lamarin da ya fusata mazauna yankin, musamman matasa.
- Xi Ya Bukaci A Samar Da Sabbin Nasarori A Fannin Habaka Masana’antu Na Gaba
- Wannan Wasika Ta Bayyana Kaunar Dake Tsakanin Sin Da Afirka
Daga nan suka yi masa dukan kawo wuƙa sannan suka ƙone shi har lahira.
An garzaya da matar zuwa wani asibiti da ke kusa domin samun kulawar gaggawa, amma zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a san halin da take ciki ba.
Daga bisani jami’an tsaro sun isa wajen tare da kama wanda ake zargin domin gudanar da bincike.
Haka kuma, an samu dawowar doka da oda bayan shigar jami’an tsaro.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun yi Allah-wadai da abin da ya faru, inda suka buƙaci jama’a da su daina ɗaukar doka a hannunsu, su riƙa miƙa duk wanda ake zargi ga hukumomin tsaro.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto rundunar ‘yansandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da lamarin.
[ad_2]
Source link