Majalisar Dokokin Ribas Ta Sake Fara Yunƙurin Tsige Fubara
[ad_1]
Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta sake fara yunƙurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga muƙaminsa.
’Yan majalisar sun fara wannan shiri ne a zaman majalisar da suka yi a ranar Alhamis, inda suka zargi Gwamna Fubara da mataimakiyarsa da aikata manyan laifukan rashin ɗa’a a game da aiki.
- Obi Na Sauya Jam’iyya Kamar ‘Yan Wasan Firimiyar Ingila – Bwala
- Harin Venezuela Ta’asa Ce Da Amurka Ke Tafkawa Tun Bayan Yakin Duniya Na Biyu
Wannan ne karo na biyu cikin watanni 10 da Majalisar ke ƙoƙarin tsige gwamnan.
A wani makamancin yunƙuri da aka yi a shekarar 2025 ne, ya sa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.
A watan Maris, ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da kuma dukkanin ’yan Majalisar Dokokin Jihar, sakamakon rikicin siyasa da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jihar.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa sun yi imanin cewa matakin da Shugaba Tinubu ya ɗauka a wancan lokaci ne ya hana aiwatar da shirin tsige Fubara.
Rikicin ya samo asali ne daga saɓanin da ke faruwa tsakanin gwamnan Fubara da tsohon ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike.
A yanzu, Fubara ya koma jam’iyyar APC, yayin da Wike har yanzu ke jam’iyyar PDP.
Sai dai Wike na jagorantar haɗin gwiwar jam’iyyu daban-daban a Jihar Ribas domin goyon bayan sake zaɓen Tinubu a shekarar 2027.
[ad_2]
Source link