Masu zanga-zangar neman tura sakamakon zabe ta intanet sun mamaye Majalisa

[ad_1]



Masu neman tabbatar da dokar tura sakamakon zabe ta intanet sun mamaye harabar Majalisar Dokoki ta Kasa domin tanadin dokar ya samu shiga.

Hakan na zuwa ne a yayin da majalisar ke shirin gudanar da zama na gaggawa kan sauye-sauyen da aka yi wa dokar zabe gabanin babban zaben 2027.

A makon jiya ne kura ta tashi bayan bullar labarin cewa majalisar ba ta amince da tura sakamakon zabe kai tsaye ta intanet ba.

A kan haka ne bangaren marasa rinjaye a majalisar suka nesanta kansu da hakan a yayin da sauran ’yan Najeriya suka tashi haikan domin ganin an tabbatar da tsarin tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar amfani da na’ura.

Yawanci ana ganin yin hakan zai takaita magudin zabe, musamman abubuwan da suka danganci aringizon kuri’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *