Gobara ta tashi a fadar Sarkin Jama’a a Kaduna
[ad_1]
Gobara ta tashi a fadar Mai Martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu, da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna.
Har yanzu ana ƙoƙarin kashe gobarar, yayin da wasu matasa suke taimakawa domin kashe wutar.
Gobarar ta lalata wani ɓangare na fadar.
A halin yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
Jami’an kwana-kwana sun isa zuwa fadar domin kashe wutar da kuma hana ta yaɗuwa, sai dai sun ce ba su da isasshen ruwa don kashe gobarar yadda ya kamata.
Cikakken bayani na tafe…
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link