Tinubu ya gana da Gwamnan Bauchi a Aso Rock

[ad_1]



Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Aso Rock a Abuja.

Ziyarar ta ja hankalin jama’a ne sa’o’i kaɗan bayan gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP APC.

Kawo yanzu Gwamna Bala Mohammed ne kaɗai ya rage a matsayin gwamnan PDP a yankin Arewa maso Gabas.

Bala, ya ce ganawar tana da alaƙa da abin da ya shafi sha’anin yin aiki tare, ba siyasa ba.

Ya bayyana cewa Jihar Bauchi na fuskantar barazanar tsaro daga ’yan bindiga, abin da ya sa wasu mazauna jihar suka bar gidajensu zuwa wasu ƙauyukan maƙwabta.

Ya ƙara da cewa ya kai rahoton ga shugaban ƙasa bayan ya ziyarci wuraren da lamarin ya shafa tare da shugabannin tsaro, inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin taimaka wa jihar.

“Ni ɗan jam’iyyar PDP ne. Ban zo nan saboda siyasa ko sauya sheƙa ba. Na zo ne domin yin haɗin gwiwa, musamman kan tsaro,” in ji Gwamna Bala.

Gwamnan, ya kuma bayyana cewa Bauchi na shirin yin taron haɗin gwiwa da jihohin makwabta domin ƙarfafa haɗin kai wajen yaƙi da laifuka.

Ya yi gargaɗin cewa matsalar tsaro na iya shafar zuba jari a fannonin ma’adinai da mai a jihar.

Bala, ya sake jaddada goyon bayansa ga kafa ’yan sandan jihohi, yana cewa hakan zai taimaka wa gwamnoni wajen magance matsalolin tsaro a yankunansu.

“Na ziyarci wuraren da lamarin ya shafa tare da shugabannin tsaro kuma na gabatar wa shugaban ƙasa rahoto. Ya ba mu tabbacin zai tallafa mana,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *