Hukumar NPA Ta Karrama Jajirtattun Matan Da Ke Aiki A Hukumar

[ad_1]

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ta shirya taro na musamman domin karrama matan da suke aiki a fannoni daban daban na hukumar, kuma aka tabbatar da gaggarumin gudummawar da suke bayarwa domin bunkasa hukumar.

Shugaban hukumar, Dakta Abubakar Dantsoho shi ne ya jagoranci zaman wanda babban makasudin gudanar da shi shi ne domin nazari da tantance irin gudummawar da mata ke bayarwa a bangaren harkokin sufurin ruwa a kasar nan.

  • Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani
  • Mataimakin Shugaba Sin Ya Gana Da Shugaban Afrika Ta Kudu Kan Dangantakar Kasashen Biyu

Wadanda suka gabatar da mukaloli daban daban a wajen zaman sun hada da Abinbola Ini Abasi da Halimatul Abdul da Bibian Richard Edett da Ayo Mairo sai kuma Kenechi Edith Okezie, dukkansu masana ne kuma kwararru a fanoni daban daban na tattalin arzikin kasa, sun kuma bijiro da bayanai masu muhimmanci na hanyoyin da za a karfafa wa mata a wannan bangaren gaba daya.

Masana sun bayyana cewa wannnan wani muhimmain mataki ne da Hukumar Tashoshin JIragen Ruwan ta dauka domin kawo kaeshen gibin da ake samu tsakanin maza da mata a wajen samu da gudanar da aiki a NPA. Haka kuma ana sa ran takardun da aka gabatar za su taimaka wajen daukaka muryoyin mata ta yadda za su kai ga matakan shugabanci a nan gaba.

Idan za a iya tunawa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta jagoranci hukumar a shekarun baya inda ta gudanar da aiki yadda ya kamata ta kuma samar da ci gaba da aka dade ba a samu irinsa ba a tarihin hukumar.

Haka kuma tun lokacin ya da dare karagar shugabancin hukumar NPA, Dakta Abubakar Dantsoho ya fito da tsare-tsare masu muhimmanci da za su kai ga samun karin mata a sassa daban daban na hukumar, abin da masana ke ganin wani abu ne da ba a taba gani ba a tarihin hukumar, a kan haka suka yaba masa tare da karfafa masa a kan bukatar ya ci gaba a kan wannan hanyar na tabbatar da daidaiton jinsi a hukumar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *