El-Rufai karatun Alƙur’ani da azumi ya dinga yi lokacin da yake tsare — Abokinsa

[ad_1]



Wani makusanci kuma abokin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana yadda tsohon gwamnan ya tafiyar da al’amuransa lokacin da yake tsare a hannun hukumomin tsaro.

Bashir Garba Sufyan, wanda aminin El-Rufai ne, ya bayyana haka. A shafinsa na X cewa tsohon gwamnan ya shagaltu da ayyukan ibada da neman ilimi yayin da yake tsare.

A cewarsa, El-Rufai ya shafe tsawon lokacin yana azumi, salloli, da kuma karatun littattafai.

Sufyan ya ƙara da cewa, tsohon gwamnan ya samu nasarar sauke Alƙur’ani mai girma gaba ɗaya, ya karanta litattafai guda 10, sannan ya rubuta wasu littattafan nasa na kansa a tsawon lokacin.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan an saki El-Rufai, inda rahotanni suka tabbatar da cewa ya riga ya isa gidansa kuma ya haɗu da iyalansa da sauran abokan arziƙi.

Idan za a iya tunawa, an kama Nasir El-Rufai ne sakamakon binciken da Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Ta’annati (EFCC) ta fara, kafin daga bisani ta miƙa shi ga Hukumar ICPC.

Hukumar ta ICPC ta gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna kan tuhume-tuhume guda 10 da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Ko da yake an ɗage sauraron buƙatar bayar xa belinsa zuwa ranar 31 ga watan Maris.

ICPC ta saki tsohon gwamnan ne biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta riga mu gidan gaskiya a birnin Alkahira na ƙasar Masar.

El-Rufai dai ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.

Ɗansa ya tabbatar da cewar ICPC ta saki mahaifinsa da yammacin ranar Juma’a.

A gefe guda kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Uba Sani, da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu, sun aike da saƙon ta’aziyyarsu ga tsohon gwamnan bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Wannan al’amari ya janyo cece-ku-ce da mabanbantan ra’ayoyi a shafukan sada zumunta, inda wasu ’yan Najeriya ke kallon tsare shi da kuma sakinsa a matsayin wani babban al’amari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *