Fitaccen Ɗan Kasuwar Kano, Bature Abdulaziz, Ya Rasu
[ad_1]
Fitaccen ɗan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Bature Abdulaziz, ya rasu.
Ya shahara wajen gudanar da harkokin kasuwanci a Kano, inda ya taɓa zama shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Kantin Kwari.
- An Damƙe Wata Yarinya Da Ta Shirya Garkuwa Da Kanta A Edo
- Ƴansanda Sun Cafke Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Kisan Wata Lauya A Abuja
Haka kuma ya kasance Shugaban Ƙungiyar Haɗin Kan ’Yan Kasuwa ta Nijeriya, inda ya yi aiki wajen tallafa wa ’yan kasuwa da bunƙasa harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar nan.
Alhaji Bature Abdulaziz ya kuma kasance Shugaban Patriotic Elders Network for Peace, wata ƙungiya da ke aiki kan zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Ɗansa, Ismail Abdulaziz ne, ya tabbatar da rasuwarsa bayan fama da rashin lafiya.
Za a yi jana’izarsa a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na safe a gidansa da ke unguwar ‘Yankaba a Kano.
[ad_2]
Source link