Bayan shekara 17, Gwamnati da ASUU sun sa hannu kan yarjejeniyar 2009
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun sa hannu kan yarjejeniya da za ta sauya tsarin biyan albashi da walwalar malaman jami’o’i wacce aka cimma a tun a shekara ta 2009.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta daidaita tsarin ilimi a manyan makarantu na Najeriya.
Tun daga shekarar 2009 ake ta tattaunawa tsakanin gwamnatin da ASUU ba tare da samun daidaito ba.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Talata, an sake nazarin albashi da alawus na malamai kuma zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.
Babban tanadi a yarjejeniyar shi ne ƙarin kashi 40 cikin 100 a albashin malaman jami’o’in tarayya.
A cewar ministan, wannan ƙarin an yi shi ne domin ƙarfafa gwiwa, inganta ayyuka, ƙara gogewa a matakin kasa da kasa, da kuma rage matsalar barin aiki da ke damun jami’o’in Najeriya.
Sabon tsarin albashi zai ƙunshi CONUASS da CATA. Gwamnati ta bayyana cewa mafi yawan ƙarin kashi 40 cikin ɗari zai fito ne daga bangaren CATA, wanda ya shafi malaman jami’a kawai.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, CATA zai kunshi muhimman kuɗaɗen aikin malamai kamar wallafa mujallu, halartar taruka, kudaden intanet, zama membobin ƙungiyoyin ilimi, da kuma alawus na littattafai.
Gwamnati ta ce waɗannan kayan aiki suna da matuƙar muhimmanci wajen koyarwa, bincike, da hulɗar ilimi a duniya.
A karon farko, Gwamnatin Tarayya ta kuma amince da alawus na musamman ga farfesoshi da wadanda suka kusa zama farfesoshin (readers).
A ƙarƙashin sabon tsari, Farfesoshi za su samu ₦1.74m a shekara (₦140,000 a wata), yayin da Readers za su samu ₦840,000 a shekara (₦70,000 a wata). Wannan alawus an tsara shi ne domin tallafawa bincike, rubuce-rubuce, mu’amala, da ingancin gudanarwa.
Ministan ya bayyana wannan mataki a matsayin “tsari mai ma’ana, mai amfani, kuma mai sauya al’amura,” yana mai cewa zai ba manyan malamai damar mai da hankali sosai kan koyarwa, jagoranci, kirkire-kirkire, da samar da ilimi a matakin duniya.
Jami’an gwamnati sun ce yarjejeniyar ta kafa tubali mai ɗorewa na zaman lafiya a jami’o’in tarayya ta hanyar magance matsalolin albashi da walwala da suka daɗe suna kawo cikas ga jadawalin karatu.
Dr Alausa ya tabbatar da cewa gwamnati za ta aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata tare da ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, yana mai bayyana wannan mataki a matsayin matakin ƙarshe na warware rikicin shekaru biyu da ya daɗe yana damun tsarin ilimi a manyan makarantu na Najeriya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link