Mutum 24 da aka sace a coci a Kogi sun kuɓuta

[ad_1]



Mutum 24 da wasu mahara suka sace a cocin ECWA da ke Jihar Kogi, sun kuɓuta.

An sace mutanen ne a ranar 14 ga watan Disamban 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari cocin da ke yankin Ayetoro-Kiri a Ƙaramar Hukumar Kabba/Bunu.

Aƙalla mutum 37 aka sace a lokacin harin.

Waɗanda aka sace sun hada da tsofaffin mata, maza da matasa.

Bayan faruwar lamarin, shugabannin al’umma tare da iyalan waɗanda aka sace sun fara tattaunawa da maharan domin ceto mutanen da aka sace.

Shugaban matasan yankin, Daniel Friday, ya ce mutane 17 daga cikin waɗanda aka sace sun kuɓuta a ranar Talata.

Wani mutum daga cikin mazauna yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a ranar 1 ga watan Janairu, 2026, an saki mutane bakwai bayan doguwar tattaunawa da kuma biyan kuɗin fansa masu yawa.

Daga cikin mutane bakwai, mutane huɗu ne kawai suka tsira da ransu, yayin da uku suka mutu.

Biyu sun rasu tun kafin a sake su, ɗaya kuma ya rasu a asibiti.

Bayan haka, an ci gaba da tattaunawa har aka saki ƙarin wasu mutane uku a ranar Litinin, sannan aka sake sakin wasu 14 a ranar Talata.

Hakan ya kawo adadin waɗanda aka sako zuwa 24 daga cikin 37 da aka sace.

Kungiyar Raya Ƙaramar Hukumar Ayetoro-Kiri Bunu, tare da haɗin gwiwar iyalan waɗanda aka sace ne, suka taka rawar gani wajen sakin mutanen.

Ƙungiyar ta ce an kashe kuɗi masu yawa wajen ganin an sake su.

Ƙungiyar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin an sako sauran mutane 13 da ke hannun ’yan bindiga, tare da roƙon jama’a su ci gaba da yin addu’o’i.

Mazauna yankin sun kuma nemi ɗauki domin tabbatar da dawowar sauran mutanen lafiya.

Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Kogi da gwamnatin jihar bai yi nasara ba, domin ba su ce komai ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

A halin yanzu kuma, ana shirin kai waɗanda aka sako asibiti a Kabba domin duba lafiyarsu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *