Juyin Mulki: Jami’an Sojoji 16 Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa
[ad_1]
Kimanin jami’an soji 16 da ake tuhuma da laifin yunKurin kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, na fuskantar hukuncin kisa ko kuma daurin rai da rai, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Hakan na zuwa ne, bayan da babban hafsan sojin kasar ya amince cewa; jami’an da ke tsare tun a watan Oktoban 2025, an same su da aikata wannan laifi.
- Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji
- Hotuna: Babbar Mota Ta Hallaka Wata Bafulatana A Bauchi
Jami’an soji da suka yi ritaya, wadanda suka zanta da jaridar Daily Trust a wata tattaunawa daban-daban a daren ranar Litinin, sun ce; dokar sojan Nijeriya ta tanadi hukuncin kisa, kan yunkurin juyin mulki.
A watan Oktoban 2025, an samu rahotannin cewa; jami’an da suka kama daga mukamin kyaftin zuwa birgediya-Janar, hukumar leken asiri ta tsaro (DIA) ta kama tare da tsare su, sakamakon yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu.
Jaridar ta ruwaito cewa, kwamitin da ya binciki jami’an da aka kama, ya mika wa shugaban kasa sakamakon bincikensa.
Daraktan yada labarai na tsaro, Samaila Uba, Manjo-Janar, ya kuma tabbatar da cewa; kwamitin binciken ya mika rahotonsa ga “hukumar da ta dace”.
Jami’an Da Za Su Fuskanci Hukuncin Kotun Soja
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Uba ya ce; za a gurfanar da wadanda ke da hannun da za su bayyana a gaban kwamitin shari’a na soja, domin fuskantar shari’a kamar yadda dokar Sojoji ta tanada da sauran ka’idojin da ake da su.
Ya ce, “Rundunar Sojin Nijeriya (AFN), na son sanar da jama’a cewa; an kammala bincike a kan lamarin, sannan kuma an mika rahoton ga hukumar da ta dace daidai da ka’idojin da aka tanada.
“Tsarin binciken da aka gudanar, bisa ka’idojin soji da aka kafa, ya yi nazari sosai kan duk wani yanayi da ya dabaibaye jami’an da abin ya shafa.
“Binciken ya gano jami’ai da dama da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnati, wanda ya saba wa ka’idoji, dabi’u da kuma ka’idojin aiki da ake bukata ga mambobin AFN.
Babban jami’in sojan ya bayyana cewa, rundunar ta bayyana wannan ci gaban a bainar jama’a, domin tabbatar da bin ka’ida tare da kiyaye ka’idojin adalci da bin doka da oda.
A cewarsa, rundunar soji ta ci gaba da jajircewa wajen kiyaye mafi girman matakan kwarewa, aminci da mutunta ikon tsarin mulki.
Uba ya kara da cewa, “AFN ta sake nanata cewa; matakan da ake dauka na ladabtarwa ne kawai, kuma wani bangare ne na ci gaba da tsare-tsare, da’a da kuma ingantaccen aiki a cikin tsari.”
[ad_2]
Source link