’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta samu rahoton laifuka 25 na cin zarafin mata da ƙananan yara a Ƙananan Hukumomin Jakusko, Fika, Potiskum da Tarmuwa, inda aka kama mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan.

Kakakin rundunar, SP Abdulkarim Dungus, ya ce an kama masu laifin ne cikin watanni uku da suka wuce, a wani yunƙuri na daƙile cin zarafin mata da yara a faɗin jihar.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani matashi mai shekara 23, Yusuf Garba, da ake zargi yi wa wata yarinya mai shekaru biyar fyaɗe.

An kai yarinyar asibiti sannan ana ci gaba da bincike a kan lamarin.

A wani lamari daban, an yi wa wata yarinya mai shekara 16 fyaɗe yayin da ta ke dawowa gida daga bikin Maulidi a Babbangida.

’Yan sanda sun kama mutum biyu; Audu Ado (22) da Babangida Alhaji Dawaye, inda suka amsa laifin bibiyar yarinyar har suka yi mata rauni.

Dungus, ya ce waɗanda abin ya shafa na samun kulawa, yayin da ake ci gaba da bincike a ofishin SCID kafin gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Ado, ya la’anci waɗannan mummunan laifuka, inda ya bayyana cewa rundunar za ta gabatar da rahoton bincikenta kafkn gurfanar da waɗanda ake zargin.

Ya kuma shawarci iyaye, shugabannin al’umma da ƙungiyoyi su ƙara kula da yara tare da haɗa kai da ’yan sanda domin kare su.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *