Capital FM Na Kenya: Taruka 2 Na Sin Suna Da Muhimmanci Ga Afirka Har Ma Da Kasashe Masu Tasowa Baki Daya
[ad_1]
Gidan rediyon Capital FM na Kenya, ya wallafa wani rahoto a kwanan nan, wanda ke cewa taron majalisar wakilan jama’ar Sin wato NPC da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na Sin wato CPPCC, suna da tasiri mai yawa ga Kenya da ma dukkan fadin nahiyar Afirka, har ma da kasashe masu tasowa na duk duniya baki daya.
A cikin rahoton, marubucinsa Stephen Ndegwa, ya ce wadannan taruka 2 na bana suna da muhimmanci na musamman, domin an gabatar da shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15 a yayin taron. Wannan shirin karo na 15 zai yi tasiri ga harkar gudanar kudaden, da bunkasar hadin gwiwar fasaha da kuma dangantakar abota ta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.
Stephen Ndegwa ya jaddada cewa, wannan yana da muhimmanci sosai ga Afirka. Sin ta dade tana kasancewa muhimmin karfi mai ingiza ci gaban duniya, kuma gudunmawarta ga ci gaban tattalin arzikin duniya ya kai fiye da kashi 30%. Idan Sin ta samu ci gaba, tsarin samar da kayayyaki zai fadada, kuma kasuwannin kayayyaki za su samu tabbaci, kana kasashe masu tasowa za su amfana saboda huldar kut da kut a bangaren hadin gwiwar kasuwanci da zuba jari tsakaninsu da Sin. Rahoton ya kuma yi amfani da bayanan cibiyoyin kasa da kasa dake cewa, duk lokacin da tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 1%, tattalin arzikin kasashen da ke da alaka da Sin zai karu da kashi 0.3%.
Stephen Ndegwa ya ce, tsarin da Sin take bi na karkata zuwa masana’antun kere-kere bisa kirkire-kirkire, da makamashi da ake iya sabuntawa, da kayan aiki na dijital ya haifar da muhimman damammaki ga tattalin arzikin Afirka. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link