Lauyoyin Gwamnatin Kano Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Rufe Ma’aikatar Shari’a

[ad_1]

Lauyoyin da ke aiki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani, inda suka ce, sakacin gwamnati na kin mayar da hankali ga jin daɗin su da wasu matsaloli kuma da aka gaza warware ne ya jefa su yajin aikin.

Jami’an shari’ar, ƙarƙashin ƙungiyar ‘Law Officers Association of Nigeria’ (LOAN) reshen Jihar Kano, sun kulle ƙofar shiga ma’aikatar da safiyar Laraba, inda suka hana ma’aikata da baƙi shiga cikin harabar ma’aikatar.

  • Majalisar CPPCC Ta Kasar Sin Ta Kammala Taronta Na Shekara
  • Ɗan Nijeriya Ya Jikkata Yayin da Iran Ta Harba Sabbin Makamai Masu Linzami Zuwa UAE

Shugaban ƙungiyar, Barrista Abdullahi Aminu Shamsu, tun da farko ya sanar da shawarar fara wannan yajin aiki, yana mai cewa gwamnati ta kasa magance matsalolin da suka dade suna addabar jami’an shari’a a ma’aikatar.

Shamsu ya ce lauyoyin na fuskantar wahalhalun yanayin aiki, kuma har yanzu akwai wasu alawus-alawus na doka da sauran hakkokinsu da doka ta tanada, ba a basu ba.

Ya ƙara da cewa, duk da tattaunawa da dama da suka yi da Gwamnatin Jihar Kano kan lamarin, har yanzu ba a magance damuwar jami’an shari’ar ba, wanda hakan ya sa suka yanke shawarar fara yajin aikin da babu ranar dakatarwa.

A cewar sanarwar da ƙungiyar ta fitar domin bayyana yajin aikin, wanda ya fara a ranar 11 ga Maris, 2026, an ɗauki matakin ne domin neman inganta jin daɗin ma’aikata, mutunta aikin lauya, kyakkyawan yanayin aiki, da kuma girmama ofishin Shari’a na jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *