Sin Ta Yi Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya


Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Sin na kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a yankin gabas ta tsakiya, tare da aiwatar da matakan shawo kan tashin hankalin da ya barke ta hanyar siyasa, kana a goyi bayan kasashen yankin Gulf wajen kare makomar yankinsu da kansu.

Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin zantawarsa ta wayar tarho da firaministan kasar Qatar, kana ministan wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani.

A cewarsa, matakin kaddamar da hare-hare da Amurka da Isra’ila suka dauka kan Iran, ba tare da amincewar kwamitin tsaro na MDD ba, ya sabawa sharudda da ka’idojin kafuwar MDD, da ma sauran matakan wanzar da alakar kasa da kasa.

A wani ci gaban kuma, kasar Sin ta nuna rashin amincewa da fadada kai hare-hare, tare da yin Allah wadai da hare-hare kan fararen hula, da wuraren da ba su shafi aikin soji ba. A cewar Wang, ya zama wajibi a martaba ikon mulkin kai, da tsaro da hurumin yankunan kasashen Larabawa dake yankin Gulf.

Har ila yau, a jiyan Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da mataimakin firaminista, kuma ministan wajen kasar Pakistan Mohammad Ishaq Dar, inda ya bayyana cewa, ginshikin kaucewa kara tsanantar halin da ake ciki dangane da Iran, shi ne Amurka da Isra’ila su dakatar da kaddamar da hare-haren soji kan kasar, kuma Sin ba ta amince da kaiwa kasashen yankin Gulf hare-hare ba, kana ta yi tir da dukkanin hare-haren da ake kaiwa kan abubuwan bukata na fararen hula, da al’ummun da ba su ji ba ba su gani ba. (Saminu Alhassan)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *