Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau
[ad_1]
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke kan hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan dogon lokacin da suka shafe ba tare da samun wutar lantarki ba.
Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Tun a watan Ramadan
Al’ummar sun bayyana cewa tun watan azumin Ramadan da ya gabata suke cikin duhu, sakamakon ƙonewar transforma da ke yankin, lamarin da ya bar su cikin ƙunci har tsawon watanni, da ke shafar rayuwar su ta yau da kullum.
Wani daga cikin mazauna yankin, Muhammad Idris Gargajiga, ya bayyana cewa duk lokacin da suka kai ƙorafi ana gaya musu cewa yankin ba shi da rumfar zaɓe, abin da ya kira da rashin adalci.
“Mafi yawanmu, kusan kashi 90 bisa 100, mun fito ne daga cikin babban birnin Gombe muka zauna a nan. Amma har yanzu ana tauye mana kallon-kallon ba ‘yan asalin yankin ba,” in ji Idris.
Ya sake yin kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da kuma ’yan siyasa da su dubi halin da suke ciki, su samar da transformer domin dawo da wutar lantarki.
Kasuwanci da walwala sun tsaya cik
Al’ummar sun ce rashin wutar ya haifar da tsaiko a harkokin kasuwanci da walwala, tare da shafar rayuwar su ta yau da kullum. Sun bukaci hukumomi su gaggauta ɗaukar mataki domin dawo da wutar yankin.
JED ba ta amsa ba
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin tuntubar hukumar samar da hasken wutar lantarki ta Jos Electricity Distribution Company (JED), wadda ke da alhakin samar da wuta a yankin, amma hakan ya ci tura.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link