Yaro mai shekara biyu ya mutu bayan ya faɗa rijiya a Kano
[ad_1]
Wani yaro mai shekara biyu, Sa’idu Ahmad, ya mutu bayan ya faɗa rijiya a garin Kwankwaso da ke Ƙaramar Hukumar Madobi a jihar Kano.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis a Kano.
Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba.
Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa daga Mataimakin Darakta na Hukumar Kashe Gobara, Rabiu Garba, da misalin ƙarfe 12:15 na rana cewa wani yaro ya nitse a rijiya, nan da nan muka tura tawagar ceto zuwa wurin.”
Abdullahi ya bayyana cewa an fito da yaron ba ya da hayyacinsa, daga bisani aka mika shi ga Umar Shehu na Sashen ’Yan Sanda na Madobi, inda ya ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin lamarin.
A wani labarin kuma, wani mutum mai shekara 28, Suleiman Sani, shi ma ya fadi rijiya a kauyen Karofawa Yan Kifi da ke Ƙaramar Hukumar Ghari.
Abdullahi ya ce wannan lamarin ma ya faru ne da yammacin ranar ta Laraba.
Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara na Ghari cewa wani mutum ya nitse a rijiya.
“Tawagar cetonmu ta garzaya wurin, an fito da mutumin ba ya cikin hayyacinsa, daga bisani iyayensa suka tabbatar da mutuwarsa.
“An mika shi ga Dagacin Karofawa, Alhaji Musa Aliyu, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.
“Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano tana mika ta’aziyya ga iyalan mamatan, tare da kira ga jama’a da su tabbatar an rufe rijiyoyi yadda ya kamata domin kauce wa irin wannan mummunan lamari,” in ji jamj’in.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link