Malami da mabiyansa sun yi sallar Idi a Sakkwato
[ad_1]
Wani malamin addinin Musulunci mazaunin Sakkwato, Sheikh Musa Lukuwa a ranar Alhamis ya jagoranci mabiyansa wajen gudanar da Sallar Idul-Fitr, a matsayin ƙalubale ga umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar, wanda ya ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar Sallah a hukumance.
Malamin ya gudanar da Sallar Idi raƙa’a biyu a masallatinsa da ke Mabera da misalin ƙarfe 9:10 na safe, bayan da rahotanni suka bayyana cewa ya yi wa mabiyansa jawabi sa’o’i kaɗan bayan sanarwar da Sarkin Musulmi ya yi na cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ko’ina a Najeriya.
A wani saƙo da ya karaɗe kafafen sada zumunta na zamani , Lukuwa ya bayyana dalilinsa na yin hakan da cewa akwai ingantattun rahotannin ganin wata a maƙwabciyar ƙasar, Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, wasu mutane da ya amince da su a ƙasar sun tabbatar da ganin watan, wanda hakan ya sa ƙungiyarsa ta ci gaba da gudanar da bikin Sallah.
“Jamhuriyar Nijar tana kusa da mu sosai—kimanin kilomita 100 ne tsakaninmu,” in ji shi. “Idan muna karɓar rahotanni daga birane kamar Kano ko ma Legas, waɗanda suke da nisa sosai, babu dalilin da zai sa mu ƙi amincewa da tabbacin ganin wata daga maƙwabciyar ƙasa.”
Ya jaddada cewa wannan mataki ba na nuna rashin mutunta hukuncin Sarkin Musulmi ba ne, ko ƙin bin koyarwar addini ne.
“Yawancin lokaci muna bin umarnin Sarkin Musulmi wajen fara azumi da ƙare shi. Sai dai idan ya fito fili cewa an ga wata, dole ne mu yi aiki da koyarwar Manzo (SAW), koda kuwa hakan ya saɓa wa sanarwar Sarkin Musulmi,” in ji shi.
Lukuwa ya kuma ya yi misali da irin rawar da marigayi Abubakar Mahmoud Gumi ya taka a baya wajen sanar da ganin wata kafin a tattara wannan alhaki a hannun Sarkin Musulmi domin haɗin kan al’ummar Musulmi.
Ya bayyana cewa shawarar da Sarkin Musulmi ya yanke a wannan karon ba daidai ba ce, kuma ya dage kan cewa mabiyansa ba za su bi wannan umarni ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link