Mene Ne Hukuncin Koyon Ilimin Taurari A Shari’a?

[ad_1]

Assalamu alaikum. Dakta, da fatan an wuni lafiya, Allah ya sa haka, amin.

Akwai wani abu mai kama da ilimi, kuma kamar tsafi ta wata fuskar. A turance, ana kiran sa ‘Astrology’, har akwai makarantun da ake koyar da darasin a Jami’o’i; kama tun daga kan digiri har zuwa digirin digirgir.

Sannan, wasu kuma na amfani da shi a matsayin sana’a; har a ƙasashen waje, ta ɓangarori daban-daban da suka haɗa da bayar da shawarwari.

  • Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Taurarin Dan Adam Na Sadarwar Intanet
  • Sin Za Ta Harba Tauraron Dan Adam Samfurin Shenzhou-22

Abin ya dogara ne kacokan a kan sanin taurari, juyawar duniya, rabe-raben ruhi da sauran makamantansu. Sun raba ruhin ɗan’adam gida huɗu, akwai; Ruwa, Ƙasa, Iska da kuma Wuta.

Ko wane ruhi yana tare da wasu taurari waɗanda ake gane su ta hanyar sanin ranar haihuwar mutum. Masu irin waɗannan ilimi, suna iya faɗan halin mutum, wanda kuma a mafi yawancin lokuta yana iya zama daidai.

Suna bayar da shawarwari game da abin da mutum zai yi, har suna faɗa wa mutum cewa, lura da taurari ko makamancin haka, yana da sa’a a wuri kaza ko kuma bashi da sa’a a wuri kaza. Suna kuma faɗar cewa, wane yana da taurarin nasara ko kuma wani abu mai kama da haka.

Ina bibiyar abin a mafi yawancin lokuta, har na fara fahimtar wasu abubuwa game da ilimin. Don haka, mene ne matsayin wannan ilimi a shari’a?

Wa’alaikum assalam. Ɗan’uwa, yin irin wannan nau’i na ilimin taurari haramun ne; yana kuma iya kai wa zuwa ga shirka, saboda Camfi ne da kuma da’awar sanin Gaibu, wanda Allah ya keɓantar da shi.

Imamu Katadah yana cewa, “Allah ya halicci taurari ne, saboda abubuwa guda uku kaɗai:

1- Gane hanya, kamar yadda Allah ya faɗa a suratu Annahl aya ta(16).

2- Ado ga saman duniya.

3- Jifan kangararrun Shaiɗanu masu sato Ji daga sama, Allah maɗaukakin sarki yana cewa a suratul Mulki aya ta (5), “Yin amfani da Taurari wajen gane Nasara ko rashinta, harka ce ta Bokaye, kuma Allah bai tanade su domin yin hakan ba; yana kuma kai wa zuwa ga halaka.

Ya halatta a yi amfani da ilmin Taurari wajen gane Alƙibla da kuma tabbatar da maslahohin addini.

Domin neman ƙarin bayani, duba Alkaulu al-mufid 2/102 da kuma Al-mulakkas fi-sharhi kitabittauhid (236).

Allah ne mafi sani.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *