Boko Haram ta sake ƙone motoci ɗauke da kayan abinci a Borno
[ad_1]
‘Yan ta’addan Boko Haram sun sake tarewa tare da ƙone wani jerin manyan motoci da ke ɗauke da kayan abinci a Jihar Borno.
Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun tare jerin tireloli da ke ɗauke da wake daga Monguno zuwa Maiduguri, a kusa da ƙauyen Burmari, cikin Ƙaramar Hukumar Guzamala.
A cewar direbobin da kuma majiyoyin tsaro, lamarin ya faru ne da safiyar Asabar, misalin ƙarfe 9:30 na safe, tsakanin kauyen Burmari da Garin Kashim.
“Mun yi imanin su ne waɗanda suka ƙone motocin kayan abinci kwanaki biyar da suka gabata. Na bar motata na gudu cikin daji. Sun tare tirela biyu da manyan motoci uku, suka ƙone kawunan tirelar sannan suka tsere cikin daji,” in ji wani direba.
Wani ganau ya ce ’yan ta’addan sun fasa tayoyin motocin kafin su ƙone su, amma an yi sa’a direbobi da suka tsira sun samu taimakon al’umma suka kashe wutar kafin ta kai ga bayan motocin.
Wasu direbobi sun koka kan rashin tsaro a hanyar, inda suka ce saɓanin wasu hanyoyi masu haɗari ba, babu sojoji a wuraren da ake yawan samun hare-hare ba a kan hanyar.
“Idan ka bi hanyar Gwoza, za ka ga sojoji a wurare daban-daban, amma wannan hanya babu tsaro. Yanzu yawancin masu motocin kaya sun janye motocinsu daga wannan hanya,” in ji wani.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan ta’addan sun fara kai hare-hare kan motocin kaya ne domin hana shirin gwamnati na mayar da al’ummomin da ke gudun hijira zuwa gidajensu.
Ta ƙara da cewa an kafa sansanin soja a yankin domin kare ’yan gudun hijira da ke son komawa garuruwansu.
A ranar 1 ga Fabrairu, 2026, ’yan ta’addan sun kashe mutum 17 a ƙauyen Abbari, da ke Ƙaramar Hukumar Guzamala.
A jiya kuma, gwamnatin Borno ta dawo da sama da ’yan gudun hijira 3,000 daga Jamhuriyar Kamaru, inda da yawancinsu ke jiran izinin sojoji kafin su koma gidajensu.
Ɗaya daga cikin yankunan da ake shirin sake zaunar da jama’a shi ne Mairari, wanda har yanzu ƙungiyar ISWAP ke da iko a shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link