Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi Bauchi

[ad_1]



Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya sun ufe makarantar a sakamakon zanga-zangar da dalibai suka gudanar domin nuna fushinsu kan harin da ’yan fashi suka kai dakunan kwanansu.

Daliban sun tayar da tarzoma ne da sanyin safiyar Talata bayan harin ’yan fashin ya ya yi sanadiyyar jikkatar wasu dalaibai da dama, suna mazu zargin hukumomin kwalejin da kasa kare su daga abin da ya faru cikin dare.

Rahotanni since ’yan fashin sun kwace wa daliban kayayyakinsu, tare da jikkata mutum tara.

An dai ga fusatattun daliban suna gudanar da zanga-zanga a kan hanyar Bauchi zuwa Dass, inda suka daura shingen hana zirga-zirga a kofar shiga kwalejin.

’Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama’a, lamarin da ya sa wasu daliban suka mayar da martani da duwatsu kafin daga bisani ’yan sanda su ci karfinsu.

Shugaban Kungiyar Dalibai (SUG) ta kwalejin, Haruna Umar, ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana shi a matsayin irinsa na farko a tarihin makarantar.

“’Yan fashin sun ji wa dalibi mai wakiltar aji daya na na matakin Difloma a fannin Kimiyyar Kwamfuta, Matta Musa rauni a kai. Wasu da suka samu raunuka an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi,” in ji shi.

Jami’in Hulda da Jama’a na kwalejin, Rabiu Wadda, ya shaida wa wakilinmu, cewa hukumar gudanarwar makarantar ta yi koqarin shawo kan lamarin kuma nan take ta rufe makarantar har zuwa wani lokaci domin hana tabarbarewar doka da oda.

Ya ce “Na kasance a makarantar tun karfe 4:00 na safe, muna kowarin shawo kan lamarin. A halin da ake ciki, ban samu shiga harabar ba.

“Yanzu, ba zan iya ba ku ainihin adadin daliban da abin ya shafa ba, amma na san an kai wasu daliban asibiti,” in ji shi.

“Hukumar gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya ta Bauchi, ta bayar da umarnin rufe harkokin ilimi a kwalejin,” a cewar wata sanarwa da aka rabawa jama’a a ranar Talata.

Magatakardar kwalejin, Kasimu Salihu, ya bayyana cewa wasu bata-gari sun mamaye dakin kwanan dalibai maza, inda suka kwashe kayansu tare da raunata kimanin dalibai biyu.

“Bayan wannan mummunan lamari, daliban sun fito daga babbar kogar kwalejin don nuna rashin jin dadinsu, suna masu kira ga hukumar da ta dauki matakin gaggawa, tare da duk manyan jami’an gudanarwa da ma’aikatan gudanarwa”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *