Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa
[ad_1]
Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan Adam da da’irarsu ke kusa da doron kasa, daga cibiyar harba kumbunan kasuwanci ta lardin Hainan dake kudancin kasar.
An harba rukunin taurarin wanda shi ne irinsa na 13, da ya kunshi jerin taurarin dan Adam masu samar da sadarwar intanet ne da misalin karfe 10:41 na safiyar yau Litinin agogon Beijing. An kuma yi amfani da rokar Long March-12 wajen harbawa, inda tuni suka shiga da’irarsu. (Mai fassara: FMM)
[ad_2]
Source link