Yanzu- Yanzu An Sako Masu Ibadar da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
[ad_1]
An saki masu ibada da aka sace daga majami’u a al’ummar Kurmin Wali, da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. An yi garkuwa da su ne a ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2026, yayin da suke halartar ibada.
Wani shugaban al’umma ya shaida wa Daily Trust cewa sakin ya faru ne a daren Laraba, inda aka ga manyan motocin suna shiga wani daji a yankin Maro tsakanin ƙarfe 11 na dare zuwa tsakar dare, kafin daga bisani su fito da mutanen da aka sace tsakanin ƙarfe 1 zuwa 2 na asuba.
- Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Titi Mai Tsawon Kilomita 35 Da Ya Haɗa Al’ummomi 76 A Kaduna
- An Sace Ƴan Kasuwa Huɗu A Wani Sabon Hari A Kaduna
Ya ce har yanzu ba a san ko an biya kuɗin fansa ko kuma an miƙa babura 17 da masu garkuwar suka nema ba. Haka kuma, bai tabbata ba ko duka mutanen da aka sace ne aka sako ba, sai dai an tabbatar da sakin wasu daga cikinsu.
Tun da farko, rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 177 aka sace a harin Kurmin Wali, inda bayan kusan makonni biyu, wasu 80 — galibinsu yara — suka tsere suka fake a dazuzzukan da ke kusa.
Sarkin Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya tabbatar da sakin mutanen tare da yabawa gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro kan ƙoƙarinsu. Ya ce waɗanda aka sako sun haɗa da yara, da mata da manya, yayin da gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
[ad_2]
Source link