Shugabar Bulgaria Iliana Yotova: Muna Begen Ganin Kamfanonin Sin Sun Kara Zuba Jari A Kasarmu

[ad_1]

A ranar 23 ga watan Janairun bana, Iliana Yotova ta zama shugaba mace ta farko ta kasar Bulgaria. Yayin da aka gudanar da taron koli na mata na duniya a watan Oktoban shekarar 2025, Iliana Yotova wadda ta zama mataimakiyar shugaban kasar Bulgaria a lokacin, ta zo kasar Sin don halartar taron tare da yin hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG.

A yayin zantawar, Iliana Yotova ta yaba wa kasar Sin domin tana da dogon tarihi da fasahohin zamani gaba daya.

Madam Yotova ta bayyana cewa, shekarar 2025 shekara ce ta cika shekaru 76 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Bulgaria da Sin, ko da yake ana fuskantar sauyin yanayi da kalubale a tarihi, kiyaye raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru 76 ya shaida cewa, kasashen biyu suna iya fahimtar juna da cimma burin samun wadata tare.

Kasashen biyu sun cimma daidaito kan bangarorin tattalin arziki, da ayyukan more rayuwa, da cinikayya, da zuba jari, da ba da ilmi, da al‘adu da sauransu. Ana iya ganin cewa, ana zurfafa dangantakar dake tsakaninsu. Kasarta ta Bulgaria tana begen ganin karin kamfanonin Sin sun zuba jari da aiwatar da ayyukansu a kasar Bulgaria. Kana kasar Bulgaria tana bin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, kuma ya kamata a yi amfani da dama tare da yin hadin gwiwa a dukkan fannoni da kuma kara zuba jari ga juna baki daya. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *