Mutum 162 aka kashe a harin Kwara – Red Cross
[ad_1]
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce adadin wadanda ’yan bindigar da suka kai hari karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara suka kashe a yanzu sun kai mutda 162.
An dai kaddamar da harin ne da yammacin Talata har zuwa wayewar garin Laraba a wani ƙauye da ke yammacin.
A baya, Gwamnan jihar ta Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya tabbatar da mutuwar mutane 75.
AbdulRazaq ya bayyana adadin ne a daren Laraba yayin da yake jawabi ga mazauna garin a fadar Sarkin Kaiama, inda ya ce waɗanda aka kashe “Musulmai ne na yankin da aka yi musu kisan gilla saboda kin mika wuya ga ’yan ta’addan da ke wa’azin wata bakuwar akida.”
Ya kuma bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da gaggawar tura bataliya ta sojoji ƙarƙashin Operation Savannah Shield domin kaddamar da martani kan maharan.
Amma Red Cross a wata sanarwa ranar Laraba, ta ce, “Rahotanni sun nuna cewa adadin mutanen da aka kashe yanzu ya kai 162, yayin da bincike na ci gaba da neman ƙarin gawarwaki,” in ji Babaomo Ayodeji, sakataren Red Cross na Jihar Kwara, wanda ya kara adadin da a baya aka ce 67 ne.
A baya, wani ɗan majalisa na yankin Kaiama, Sa’idu Baba Ahmed, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP) cewa an kirga “gawarwaki 35 zuwa 40” daga harin da aka kai da yammacin Talata.
’Yan sanda sun tabbatar da harin amma ba su bayar da adadin mutanen da suka mutu ba, yayin da gwamnatin jihar ta dora alhakin harin kan ƙungiyoyin ta’addanci.
Ahmed ya ce, “da dama sun tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga,” yana mai ƙara da cewa ana iya gano ƙarin gawarwaki daga baya.
Ya ce maharan sun kutsa ƙauyen Woro da misalin ƙarfe 6 na yamma, suka ƙone shaguna da fadar sarkin garin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link