Me Ya Haifar Da Abubuwan Bakin Cikin Da Ke Faruwa A Minneapolis
Daga “mutuwar Renée Nicole Good” zuwa “mutuwar Alex Pretti “, a wuraren da nisansu bai wuce kilomita 2 ba, a cikin kwanaki 17 kawai, hukumar kula da shige da fice da yaki da fasakwabri ta tarayyar Amurka wato ICE ta kashe rayuka biyu a jere.
Inda aka kashe Renée Nicole Good da inda aka halaka George Floyd a kusan shekaru 6 da suka gabata, nisansu bai wuce kilomita 2 ba. Cikin sama da shekaru 5 da suka gabata, yadda ‘yan sandan kasar Amurka suka sha nuna karfin tuwo a yayin aiwatar da ayyukansu yana ci wa al’ummar kasar Amurka tuwo a kwarya .
Harbe-harben bindiga sun shaida matsalolin da al’ummar kasar Amurka ke fuskanta, kuma da wuya a kai ga daidaita matsalar nuna karfin tuwo da ‘yan sandan kasar kan yi a lokacin da suke aiwatar da ayyukansu, duba da yadda ake fama da wariyar launin fata da rarrabuwar kawuna da karuwar gibi a tsakanin masu kudi da matalauta da yawaitar makamai da sauransu. A lokaci guda, irin wadannan matsalolin suna kara sa jam’iyyun Republican da Democrat su nuna yatsa ga juna, don neman fa’idodin siyasa.
Amurka ba za ta samu cikakken kwanciyar hankali ba, har sai an warware wadannan matsalolin da ake fuskanta a kasar. (Mai zane da rubutu: MINA)