Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki Sun Yi Fatali Da Shirin Gwamnati Na Ba Da Mita Kyauta

[ad_1]

Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun nuna shakku kan umarnin da Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayar cewa dole ne a rika bai wa dukkan rukunin kwastomomi mitocin wuta kyauta.

Masu gudanar da kamfanonin, wadanda suka yi magana da wakilinmu ba tare da bayyana sunayensu ba saboda la’akari da mahimmancin batun, sun ce ministan ya yi furuci na siyasa ne kawai, ba tare da yin la’akari da ra’ayoyin sauran masu ruwa da tsaki ba, musamman masu makala mitoci da kamfanonin samar da mitoci.

  • Za A Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Na Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Birnin Beijing
  • Raheem Sterling Ya Bar Chelsea Bayan Shafe Shekaru 3

A ranar Alhamis, Gwamnatin Tarayya ta haramta wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da masu makala mitoci karbar kowane irin kudi daga kwastomomi kan batun mita, tana mai gargadin cewa duk wani jami’in DisCo ko mai sanya mita da aka samu yana karbar kudi ko cin zarafin kwastomomi za a gurfanar da shi a gaban shari’a.

Adelabu ya bayar da wannan gargadi ne yayin wani bincike kai tsaye da ya kai kan sabbin mitocin zamani (smart meters) da aka shigo da su kasar, a APM Terminals, Apapa, Jihar Legas.

Adelabu ya ce, an samar da mitocin ne karkashin Shirin Farfado da Bangaren Rarraba Wutar Lantarki (Distribution Sector Recobery Programme) da Bankin Duniya ke daukar nauyi, kuma dole ne a sanya su ga kwastomomi kyauta, yana jaddada cewa duk wata bukatar kudi za a dauke ta a matsayin laifi.

Ya ce za a raba mitocin ga dukkan kwastomomin wutar lantarki, ba tare da la’akari da rukunin (band) da suke ciki ba.

“Ina so in bayyana cewa wannan abu ba a taba yin irinsa ba, domin za a sanya tare da rarraba wadannan mitoci ga kwastomomi kyauta gaba daya! Kada wani ya karbi kudi daga kowane kwastoma. Wannan haramun ne kuma laifi ne. Haramun ne ga jami’an kamfanonin rarraba wutar lantarki a fadin Nijeriya su nemi ko sisi guda kafin a sanya mita; har ma masu makala mitocin da ba na kai tsaye ba ba su da ikon karbar ko sisi guda daga kwastomomi. Dole ne a makala mitocin kyauta domin a inganta lissafin kudin wuta da kuma tarin kudaden shiga ga bangaren,” in ji Adelabu.

Sai dai kuma, masu gudanar da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da suka yi magana da The PUNCH sun ce mitocin da Gwamnatin Tarayya ta ayyana a matsayin kyauta za a biya kudinsu ne daga hannun DisCos cikin tsawon shekaru 10.

Masu gudanarwar sun shaida wa wakilinmu cewa ba zai yiwu DisCos su zama masu daukar nauyin makala mitocin ba, suna tambayar dalilin da ya sa gwamnati ke son dora musu kudin makalawa.

A cewarsu, masu makala mitoci ba ma’aikatan DisCo ba ne, don haka dole ne wani ya dauki nauyin kudin makalawa.

“Wadannan mitoci da kuke gani, dole ne wani ya biya kudinsu. Gwamnati na tsammanin DisCos su dauki nauyin wadannan mitoci da ake kira kyauta. Sun ce DisCos za su iya biyan kudin cikin shekaru 10.

“Idan aka umarci DisCos su biya kowane irin kudin zuba jari, ana kiran hakan allowable caped. Dole ne a amince da shi yayin lissafin farashin wutar lantarki (tariffs); in ba haka ba, hakan zai sa takardun kudin kamfanonin su lalace,” in ji wani jami’i daga daya daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki.

Wani daga cikin masu gudanar da DisCo ya ce, “Ya kamata mu fahimci cewa masu makala mitoci ba ma’aikatan DisCos ba ne. Tuni sun fara tambayar waye zai biya su idan kwastomomi ba su biya ba.

Shin ministan ya yi la’akari da duk wadannan abubuwa? Kun ce mutane ba za su biya masu makala mitoci ba; to waye zai biya su? Mu DisCos ba mu ne ke makala mitoci ba. An kwace wannan aiki daga hannun DisCos tun lokacin da Babatunde Fashola yake Ministan Wutar Lantarki.

“Sun ce DisCos ba su da wani aiki da batun mitoci. Wannan ne sakamakon da muke gani a yau. Da a ce DisCos su ne ke makala mitoci, za a iya tilasta musu su biya kudin. A kwanaki masu zuwa za mu ga sakamakon wannan furuci. Idan gwamnati za ta iya biyan masu makala mitoci, babu matsala, amma ban tabbatar da cewa akwai wani DisCo da zai yarda ya dauki nauyin biyan masu makala mitoci ba.”

Jami’an sun bayyana kalaman Adelabu a matsayin furuci na neman farin jini daga dan siyasa.

“Wannan magana furuci ne kawai na neman farin jini daga dan siyasa. Ba mu tabbatar ko Shugaban Kasa ne ya ba shi wannan sako ba. Ya ce komai ya zama kyauta; to ina batun dawo da kudin da aka kashe? Duk abin da za ka yi a bangaren wutar lantarki, dole ne ka fara tunanin waye zai dauki nauyin kudin. Dole ne wani ya dauki nauyin don kauce wa taruwar bashi.

“Ya dace gwamnati ta zauna da DisCos da masana’antun kera mitoci domin neman shawarwari, idan manufar ita ce mutane kada su dauki kowane irin kudi, mu kuma mu fito da tamu gudummawar.

Amma maimakon haka, gwamnati za ta fita ta yi alkawura marasa tushe ga jama’a. Alal misali, ana shigo da mitocin ne a rukuni-rukuni, amma an sa jama’a su yi tunanin cewa mitoci sun wadatar ga kowa. Wannan ba shi ne gaskiyar lamarin ba,” in ji daya daga cikin majiyoyin.

Masu gudanar da kamfanonin sun kara da cewa ayyana mitoci a matsayin kyauta zai iya lalata tsarin (MAP), wanda ke bai wa mutane damar sayen mitoci idan suna bukatarsu.

“Yanzu mutane suna kin karbar tsarin MAP saboda sun ji cewa mitoci kyauta ne. Ministan ya fito da labari mara kyau. Shin ya zauna da masu ruwa da tsaki kafin ya fito ya ce mitoci kyauta ne?

Ta yaya za ka ce kana da isassun mitoci ga fiye da mutane miliyan biyar? Har yanzu muna da tsarin MAP da ke gudana, inda mai samar da mita ke sayar wa kwastoma kai tsaye. MAP har yanzu yana nan saboda mitocin kyauta da ake shigowa da su ba za su iya cike gibin rashin mita ba.

“Saboda haka, MAP yana tafiya ne a lokaci guda tsawon shekaru. Amma wannan sabon bayani yanzu yana shafar MAP, domin mutane ba su fahimci bambanci ba. Ya kamata gwamnati ta yi karin bayani dalla-dalla ta kuma sanar da jama’a cewa mitocin kyauta ba za su wadatar ga kowa ba; ya kamata ta bayyana wuraren da za a raba mitocin kyauta da kuma rukunin kwastomomin da za su amfana.

Ta haka, wadanda ba su shiga cikin shirin ba za su san cewa dole ne su koma tsarin MAP ta hanyar sayen mita da kudinsu, sannan daga baya a mayar musu da kudin ta hanyar ragin kudin wuta (energy credits) a hankali,” in ji masu gudanarwar.

“Amma da furucin minista na cewa mitocin kyauta na dukkan kwastomomi ne, babu wanda zai sake bin tsarin MAP, kuma ban san yadda hakan zai shafi masu samar da mitoci na cikin gida a karkashin tsarin MAP ba,” in ji daya daga cikin masu gudanar da DisCo.

Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati da kuma hukumar da ke kula da harkokin wutar lantarki (regulator) da su rika la’akari da batun dawo da kudin da aka kashe a duk wani tsari da za su yi.

“Idan ya ce kada a biya masu makala mitoci, to waye zai biya su? DisCos ne ko Ma’aikatar Wutar Lantarki? Wadannan su ne tambayoyin da ya kamata gwamnati ta amsa. Hukumar kula da harkokin ya kamata kullum ta rika magana kan. Daga yadda al’amura suke, ministan bai nuna yana damu sosai da batun dawo da kudin da aka kashe ba, kuma yana jin dadin yin furucin siyasa.

“Dole ne ya bayyana mana waye zai biya. Mun yarda, kada mutane su biya, babu matsala, amma waye zai biya? Shin za a sake ba da tallafi (subsidy) ne? Ko gwamnati ce za ta biya? Idan gwamnati ta ce masu gudanarwa su biya, to ina za su samo kudin da za su mayar da su?

Kowane kobo dole ne a lissafta shi a kuma dawo da shi. Manufar kasuwanci ita ce dawo da kudin da aka kashe; idan ba za ka iya dawo da kudin ba, dole ne ka fara rage inganci ko yin abin da bai dace ba,” wani daga cikin masu gudanarwar ya jaddada.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *