Sin Ta Samu Gagarumin Ci Gaban Makamashin Dake Iya Sabuntawa Inda Ya Kai 60% A Shekarar 2025
[ad_1]
Makamashin dake iya sabuntawa ya kai fiye da kashi 60 cikin dari na jimillar karfin wutar lantarki da kasar Sin ta samar a shekarar 2025, wanda hakan ke nuna yadda kasar ke hanzarta sauyawa zuwa samar da ci gaba mara gurbata muhalli da ke rage fitar da hayakin carbon, kamar yadda hukumar makamashi ta kasar (NEA) ta sanar a yau Jumma’a.
A cewar NEA, kasar Sin ta kara karfin janyo wutar lantarki ta iska da hasken rana sama da kilowatt miliyan 430 a shekarar da ta gabata, wanda hakan ya kawo jimillar karfin wutar lantarki daga iska da hasken rana da aka samar zuwa adadin kilowatt biliyan 1.8.
Bugu da kari, janyo wutar lantarki daga hanyoyin samar da makamashin dake iya sabuntawa ya kai kimanin sa’o’in kilowatt tiriliyan 4 a shekarar 2025, inda hakan ya kara nuna ci gaba mai muhimmanci da irin rawar da makamashi mai tsafta yake takawa a cikin tsarin samar da wutar lantarki da aka gauraya a kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link