ADC Ta Gargadi APC Kan Tilasta Wa Ma’aikatan Gwamnati Yin Rijistar Jam’iyyar

[ad_1]

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi gargadi kan rahotannin da ke cewa ana tilasta wa ma’aikatan gwamnati da ma ma’aikatan jihohi a sassa da dama na ƙasar yi rijista da jam’iyyar APC saboda siyasa.

A wata sanarwa da Mallam Bolaji Abdullahi, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na ADC, ya fitar a ranar Lahadi, jam’iyyar ta ce an samu rahotanni masu yawa daga jihohi da dama inda ake ƙoƙarin matsawa ma’aikatan gwamnati lamba su shiga cikin tsarin rijistar APC.

  • ADC Ta Gargadi Magoya Bayan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Gabanin Zaben Fitar Da Gwani
  • Ƙwace Mulki A Hannun Tinubu Ne Kaɗai Hanyar Ceto Nijeriya A 2027 — ADC

Jam’iyyar ta bayyana wannan abin a matsayin wani ƙoƙari da ake danganta shi da shugabancin ƙasa na APC, inda ake amfani da matsin lamba ta fuskar aikin yi domin tilasta wa mutane su yi rajista.

ADC ta ce tilasta wa ma’aikata su shiga jam’iyya ba abin karɓa ba ne a cikin al’umma mai dimokiraɗiyya, domin hakan na karya ‘yancin ɗan ƙasa na zabar jam’iyyar da ya so da kuma ‘yancin sauran mutane.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa abin da ake kira e‑registration a halin yanzu yana kama da tilastawa ta fuskar tattalin arziki da jan hannu, wanda zai iya zama barazana ga ƙwarewar ma’aikatan gwamnati da kuma nuna son kai.

Jam’iyyar ta kuma kira hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Hukumar Kare Bayanan Sirri na Nijeriya (NDPC) da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da ƙungiyoyin matasa da kungiyoyin ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki da su sanya ido sosai kan abin da ta ce zai iya zama tauye hakkin ‘yancin ɗan adam da sirrin bayanai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *