Sanatan Nasarawa Ta Arewa, Godiya Akwashiki, Ya Rasu Yana Da Shekaru 52
[ad_1]
Godiya Akwashiki, Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Arewa a Jihar Nasarawa, ya rasu.
Ya rasu a ranar Laraba a ƙasar Indiya bayan fama da rashin lafiya mai tsanani, ya rasu yana da shekaru 52 a duniya.
- Ba Ni Da Alaƙa Ko Hannu A Ta’addanci – Gwamnan Bauchi
- ‘Yan Bindiga Sun Rage Kuɗin Fansar Matafiya 28 Da Suka Sace A Filato zuwa N30m
Ba a samu tabbaci daga iyalinsa ko gwamnatin Jihar Nasarawa ba, amma labarin rasuwarsa ya yaɗu a shafukan sada zumunta.
Sanata Akwashiki, ya daɗe da daina shiga cikin jama’a saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
Wata majiya ta ce, duk da cewa ya daɗe yana rashin lafiya, labarin rasuwarsa ya girgiza su.
Majiyar ta ƙara da cewa Akwashiki ya taimaki mutane da dama a mazaɓarsa ba, da kuma faɗin Jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya.
Rasuwarsa babban rashi ne ga al’ummar Eggon.
Kafin rasuwarsa, shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Hulɗar Majalisu da kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Kafafen Watsa Labarai da Harkokin Jama’a.
An haifi Akwashiki a watan Agustan 1973.
Ya fara harkar siyasa a 2011 lokacin da aka zaɓe shi a ɗan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ƙarƙashin jam’iyyar PDP, inda ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar.
A zaɓen 2015, an sake zaɓensa kuma ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar.
A 2019, ya lashe kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Bayan rasa tikitin takara a APC, ya koma jam’iyyar SDP kuma ya sake lashe kujerarsa a 2023.
Sanata Akwashiki yana da aure da ‘ya’ya.
[ad_2]
Source link