Sanata Akwashiki ya rasu a ƙasar Indiya

[ad_1]



Sanata Godiya Akwashiki, wanda ke wakiltar Nasarawa ta Arewa, ya rasu yana da shekara 52 a wani asibiti a ƙasar Indiya.

Sanatan ya daɗe yana fama da rashin lafiya, inda yake ziyartar Indiya don neman magani.

An haifi Akwashiki a ranar 3 ga watan Agustan 1973, a Angba Iggah, Nasarawa Eggon.

Ya yi aiki a wurare daban-daban kafin daga bisani ya zama ɗan siyasa.

Kafin ya zama Sanata a shekarar 2019 ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya riƙe muƙamin Shugaban Marasa Rinjaye da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa.

An sake zaɓarsa a matsayin Sanata a shekarar 2023 a jam’iyyar SDP.

Hadimin Sanata Ajegena, Likita Ibrahim ne, ya tabbatar da rasuwar Akwashiki.

Hadimin ya ce suna tuntuɓar iyalan Akwashiki a Indiya, amma har yanzu ba a fara shirye-shiryen dawo da gawarsa Najeriya don yi masa jana’iza ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *