Jihar Kogi Ta Ƙaddamar Da Masu Ba Da Taimakon Fasaha

[ad_1]

Kwamishinan ilimi na Jihar Kogi, Wemi Jones, ya buɗe horarwa kan lamarin daya shafi muhalli da yadda abin yake da alaƙa da fasahar samar da abubuwan taimakawa al’umma a ƙarƙashin tsarin koyarwa na ƴanmata da basu tallafin dogaro da kansu duk dai a ƙarƙashin tsarinh (AGILE).

Horarwar AGILE ce ta Kogi ta shirya shi,a matsayin tsarin da ake yi na taimakon gyaran makaranta na tsare- tsaren Bankin duniya.

  • Jami’an Tsaro Sun Kashe Dan Ta’adda, Kachalla Kabiru A Jihar Kogi
  • EFCC Ta Gabatar Da Ƙarin Hujjoji A Shari’ar Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello

Kamar yadda Kwamishinan ya ce, an shirya ita horarwar ne domin tabbatar da ana bin tsarin dokoki na kulawa da muhalli,domin bunƙasa shigar al’umma cikin abubuwan da za su amfane su.

Sauran abubuwan sun haɗa da ƙara bunƙasa yadda za ‘a riƙa bibiyar yadda ake tafiyar da ayyukan kamar yadda tsarin Bankin duniya ya amince da a aiwatar.

Ya ce manufar tsarin AGILE ita ce ya bunƙasa samar da ingantaccen ilimi ga ƴanmata,ta hanyar gyarawa da ɗaukaka abubuwan more rayuwa da zasu sa a samu damar tafiyar da harkokin koyarwa da koyo,shi ma irin yanayin na yadda za’a koyar mafi dacewa tare da bunƙasawa,da bada dama ta hanyoyi daban daban na samun ilimi a faɗin Jihar.

“Tsarin ya bayyana aniyar gwamnatin Jihar Kogi ita ce samar da ingantaccem ilimi wanda zai taimaka wajen gyaran da ake son kawowa ta ɓangaren ilimi kamar dai yadda ya yi ƙarin bayani,”.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *