Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

[ad_1]


Rahotanni sun bayyana cewa wani Laftanar Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya, Lt. A. M. Yarima, wanda aka gan shi cikin wani bidiyo kwanan nan yana cece-kuce da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a kwanakin baya, ya tsira daga wani yunƙurin kashe shi a daren Lahadi a Abuja. Majiyoyin Soja sun shaida wa Jaridar Vanguard cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba, sanye da baƙaƙen kaya, a cikin manyan motoci biyu ƙirar Hilux ba tare da lambar mota ba, sun biyo shi.

A cewar majiyar, motocin sun bi Yarima tun daga tashar mai ta NIPCO da ke Line Expressway har zuwa Gado Nasco Way. Bayan ya lura ana binsa, jami’in ya yi dabara ta musamman wadda ta taimaka masa ya kauce wa masu bibiyar tasa, lamarin da ya faru kusan ƙarfe 6:30 na yamma. An ce an fara bincike kan al’amarin, kuma ba za a fitar da ƙarin bayani nan ba da jimawa ba domin kada a lalata tsarin binciken.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin Yarima da Minista Wike a wurin filin da ake cece-kuce a Gaduwa. Bidiyon wannan takaddama ya yaɗu sosai a yanar gizo, ya jawo cece-kuce a faɗin ƙasar, kuma ya sa fadar shugaban ƙasa ta dakatar da rusau a wurin.

Bayan faruwar haka, tsofaffin Sojoji a sassa daban-daban sun yi tir da kalaman Wike kan jami’in, tare da gargaɗin cewa za su mamaye ofishin da gidan ministan idan aka yi yunƙurin hukunta Yarima. Ƙungiyar tsofaffin Sojojin ta jaddada cewa doka da ƙasa su kaɗai Sojoji ke bi, ba son rai ko umarnin wani jami’in gwamnati ba.

Ministan Tsaro, Mohammad Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa babu wani jami’in da zai fuskanci hukunci muddin yana aiwatar da aikinsa bisa doka. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da kare dukkan jami’an tsaron da ke yin aikinsu cikin gaskiya da ladabi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *