Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Makarantar Koyar Da Harsuna A Kano
Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar Bankin Raya Musulunci (IsDB) sun ƙaddamar da makarantar koyar da tsarin harsuna biyu (Turanci da Larabci) a Ƙaramar Hukumar Kiru ta Jihar Kano, domin ƙara samun ingantaccen ilimi ga yara.
A wajen bikin ƙaddamarwar, Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta ce makarantar za ta taimaka wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma yara masu rauni.
- Nasarorin Kasar Sin Manuniya Ce Cewa, Abun Da Hakuri Da Sanin Ya Kamata Bai Kawo Ba, Nuna Karfi Ba Zai Kawo Ba
- He Lifeng Ya Halarci Taron WEF Tare Da Ziyartar Kasar Switzerland
Ta bayyana cewa makarantar na koyar da Turanci da Larabci tare da dabarun sana’o’i, fasahar zamani (ICT) da hanyoyin koyarwa na zamani.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce makarantar za ta samar da sabbin damammaki na ilimi tare da ƙarfafa gyaran ɓangaren ilimi da ake yi a jihar.
Sakatariyar Zartarwa ta UBEC, Aisha Garba, ta ce makarantar Kiru na daga cikin makarantu 30 na tsarin koyon harsuna da ake ginawa a jihohi tara, inda Kano ce ta huɗu daga cikinsu.
Ta ƙara da cewa kowace makaranta na ɗaukar sama da ɗalibai 1,000 tare da ɗakunan karatu, masauki da sauran muhimman kayayyaki.