ADC ta dakatar da shugabanta a Nasarawa
[ad_1]
Jam’iyyar ADC a Jihar Nasarawa, ta dakatar da shugabanta na jihar, Godwin Alaku Williams, bisa zargin aikata wasu abubuwa da suka saɓa wa dokokin jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Idris Ojoko, ya ce an ɗauki matakin ne bayan samun wata takarda ƙorafi da ke zargin Alaku da ayyukan da ke barazana ga haɗin kai da cigaban jam’iyyar.
Zarge-zargen sun haɗa da ƙin amincewa da shugabancin jam’iyyar na ƙasa, ƙin haɗa kai don yin haɗaka, da kuma kai rahoton shugabannin jam’iyyar ga hukumomin tsaro.
An ce an dakatar da Alaku na tsawon kwanaki 14 domin a gudanar da bincike ta hannun kwamitin ladabtarwa.
An naɗa Barista Paul Magaji Ajeh a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar na jihar, yayin da Umar Babayaro ya zama muƙaddashin sakatare.
Sai dai Alaku ya yi watsi da matakin dakatarwar.
Ya ce waɗanda suka ɗauki matakin ba cikakkun ’yan jam’iyyar ba ne, tare da zargin su da yunƙurin kawo wa ADC cikas gabanin zaɓen 2027.
Ya jaddada cewa har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar na jihar har zuwa ƙarshen wa’adinsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link