Ina Cikin Masu Neman Horar Da ‘Yan Wasan Nijeriya Yan Ƙasa Da Shekaru 17 – Sani Kaita
[ad_1]
Tsohon dan wasan Nijeriya Sani Kaita na daga cikin wadanda ke neman aikin horar da yan wasan Nijeriya yan kasa da shekaru 17 da ake yiwa lakabi da Golden Eaglets, Kaita wanda ya wakilci Nijeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2010, ya nuna kwarin gwiwa sosai kan kwarewarsa ta horar da yan wasa.
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) kwanan nan ta bayyana cewar tana neman wanda zai karbi aikin horar da yan wasan tawagar kwallon kafar kasar yan kasa da shekaru 17, Sani Kaita wanda a halin yanzu yake zaune a kasar Birtaniya, ya bayyana cewar kwarewar da ya samu a wasannin da ya buga a kungiyoyin kwallon kafa na Turai da suka hada da Sparta Rotterdam da Monaco, tareda lasisin horarwa na UEFA B da yake dashi ka iya zama abin dubawa yayin duba cancantarshi.
“Ina tabbatar maku da cewa na nemi aikin horar da matasa yan kasa da shekaru 17,” in ji Kaita, wanda ya lashe kyautar azurfa a gasar cin kofin Duniya ta FIFA ta yan kasa da shekaru 20 a shekarar 2005 da kuma gasar Olympics da akayi a birnin Beijing na kasar China a shekarar 2008, ya cigaba da cewa “Lokaci ya yi da zan bayar da gudunmawa ta wajen bunkasa yan wasanmu matasa a cikin yanayi mai kyau da inganci”.
[ad_2]
Source link