An Yi Bikin Nuna Al’adun Gargajiya Na Bikin Bazara Na Kasar Sin A Kasar Angola
[ad_1]
Daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa ranar 1 ga watan Fabrairun da muke ciki, kungiyar kamfanonin kasar Sin dake kasar Angola, da babbar kungiyar ’yan kasuwan kasar Sin dake Angola sun dauki nauyin gudanar da bikin nuna al’adun gargajiya don murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar kasar Sin wato Bikin Bazara a birnin Luanda, karkashin jagorancin ofishin jakadancin kasar Sin dake Angola, gami da gwamnatin birnin Ingombota na lardin Luanda.
Jakadan kasar Sin a Angola, Zhang Bin, da ministan al’adu na kasar, Filipe Silva de Pina Zau sun halarci bikin, inda kuma aka gabatar da shirin talibijin mai tallata shagalin murnar Bikin Bazara na CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, al’amarin da ya isar da sakon gaisuwar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin.
Jakada Zhang Bin ya ce, 2026, shekara ce ta musanyar al’adu da cudanyar al’umma tsakanin Sin da Afirka. Bikin da aka yi a wannan karo ya kasance bikin nuna al’adu mai kayatarwa na farko bisa hadin-gwiwar Sin da Angola karkashin wannan jigo, da nufin baiwa al’ummar Angola damar kara fahimtar nagartattun al’adun gargajiyar kasar Sin.
Kasar Sin tana fatan ci gaba da zurfafa hadin-gwiwa tare da Angola, a bangarorin da suka shafi musanyar al’adu, da cudanyar matasa, da kara horas da kwararru. (Murtala Zhang)
[ad_2]
Source link