Iran ta tabbatar da mutuwar jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei
[ad_1]
Iran ta tabbatar da cewa an kashe jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan ƙasar a ranar Asabar.
Wannan na zuwa ne bayan an yi ta musanta mutuwar jagoran addini wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya shelanta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.
Sai dai kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta ce an kashe jagoran, lamarin da ya sanya kiraye-kiraye ga rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards domin ta ɗauki matakin ramuwar gayya.
Gidan talbijin na ƙasar Iran ranar Lahadi ya sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai bayan kisan shugaban addinin ƙasar mai shekara 86, wanda ke kan mulki tun shekarar 1989.
Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa a kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin.
“Shahadar da shugaban addini ya yi ba za ta sa a manta da tafarkinsa da jagorancinsa ba, hasali ma, za a tabbatar da su ne bisa ƙarfin gwiwa da jajircewa,” a cewar mai gabatar da labarai a gidan talbijin na gwamnatin Iran.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link