Ɗaliba ta rasu a ƙoƙarin duba sakamakon jarabawarta

[ad_1]



Wata ɗaliba ’yar shekara 16 ta rasu a sakamakon ambaliya a hanyarta ta zuwa duba sakamakon jarabawarta ta kammala sakandare.

Praise Malachi, ɗaliba a ajin karshe na Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Samaru, Zariya, ta samu tallafin karatu daga Cibiyar Ilimi ga ’Yan Mata da ke Zariya, saboda hazaƙarta a fannin karatu.

Mahaifinta, Emmanuel Malachi, ya bayyana cewa Praise ta gamu da ajalinta ne a hanyarta ta zuwa gida domin duba sakamakon jarabawarta, bayan da abokan karatunta suka shaida mata cewa ta yi fice sosai.

Ya ce, “Da misalin ƙarfe 6 na yamma bayan ruwan sama, abokan Praise suka zo shagona suka shaida mata cewa sakamakon SSCE ya fito kuma ta yi matukar ƙoƙari, shi ne ta yi gaggawar komawa gida domin duba sakamakon a wayarta.

“Yayin da take ƙoƙarin ƙetare wani ƙaramin kogi da ambaliya ta haifar sakamakon zaizayar ƙasa, ta zame, ta faɗa cikin ruwan kuma ambaliya ta tafi da ita.

“Sai washegari aka gano gawarta a Hunkuyi, Ƙaramar Hukumar Kudan,“ in ji shi.

Wasu maƙwabcinsu, suna Ɗanladi Mudi da Emma Yashi sun bayyana cewa guguwa da zaizayar ƙasa  sun ƙara tsananta ambaliya a yankin, lamarin da ke haddasa taruwar ruwa mai yawa yayin ruwan sama.

“Ba Praise kaɗai ba ce ta rasa ranta a wannan kogi. An sha rasa rayuka a baya sakamakon matsalar zaizayar kasa,“ in ji su.

Yayin da take magana kan wannan iftila’i, Habiba Mohammed, Daraktar Cibiyar Ilimi ga ’Yan Mata, ta bayyana Praise a matsayin daya daga cikin dalibansu mafiya hazaƙa.

“Mutuwarta ta girgiza mu matuƙa. Praise yarinya ce mai hazaƙa da tarbiyya, kuma tana da kyakkyawar makoma. Ta riga ta samu tallafin karatu domin ci gaba da karatu,” in ji ta, yayin da take jajanta wa iyalan dalibar.

Ta roƙi hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakin gaggawa wajen magance matsalar zaizayar ƙasa da kuma gina gada a wurin, domin kare rayukan al’umma.

Zariya na fuskantar ambaliya a kai a kai a ’yan shekarun nan. A ranar 27 ga watan Agusta, 2024, ambaliya ta shafi gidaje sama da 200, ta lalata makarantar firamare ta gwamnati, tare da rushe wani ɓangare mai yawa na maƙabartar Hayin Ojo.

Al’umma na ci gaba da roƙon gwamnati da masu hannu da shuni da su kawo ɗauki cikin gaggawa.

Masana sun ce dole ne a ɗauki matakan dogon lokaci domin rage illar ambaliya da kare rayukan jama’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *