An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce

[ad_1]

An gudanar da taro a jiya Alhamis, inda aka bayyana nasarorin da kasar Sin ta cimma ta fannin inganta ayyukan sadarwa tare da bayar da rahoton ci gaban ayyukan gwamnati ta yin amfani da hanyoyin sadarwa na zamani, tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2025, bisa aiwatar da shirin raya kasa da shekaru biyar-biyar karo na 14. Bisa labarin da aka samo, an ce, cikin shekaru biyar da suka wuce, an yi matukar inganta harkokin sadarwa a kasar Sin, inda yawan mutanen da ke amfani da yanar gizo ya karu daga kaso 70.4% zuwa 79.7%, an kuma rage gibin da ke tsakanin birane da karkara ta wannan fanni da kimanin kaso 8.2%, kwatankwacin lokacin da aka aiwatar da shirin raya kasa karo na 13, wato tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, har ma yawan amfani da fasahohin sadarwa na zamani wajen gudanar da ayyukan gona ma ya karu daga kaso 22.5% zuwa 30%. (Lubabatu Lei)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *