Ɓata-gari Sun Kashe Matar Aure Da ’Ya’yanta 3 A Kano
[ad_1]
Wasu da ba a san ko su wane ba sun kashe wata matar aure da ’ya’yanta uku a gidansu da ke unguwar Chiranchi Dorayi a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 17 ga watan Janairu, 2026, lamarin da ya girgiza mazauna yankin.
- Sin: Tattaunawa Da Diplomasiyya Na Da Muhimmanci Wajen Samun Zaman Lafiya Mai Dorewa
- Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Shafe Makonni A UAE Da Turai
Mutanen unguwar sun ce wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kashe matar da ’ya’yanta.
Sun kuma ce an jefa jaririn matar a cikin rijiya.
’Yansanda sun isa wurin kuma sun fara bincike.
Har yanzu babu cikakken bayani game da lamarin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yansandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura.
[ad_2]
Source link