Amurka ta tabbatar da tura sojojinta zuwa Najeriya
[ad_1]
Ƙasar Amurka ta me motsi wata karamar rundunar sojoji zuwa Najeriya bayan sabuwar yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro da ta kulla tsakaninta da Najeriyar.
Kwamandan da ke jagorantar rundunar Amurka a nahiyar Afirka (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata.
Wannan shi ne karo na farko da aka tabbatar da kasancewar sojojin kasa na Amurka a cikin Najeriya tun lokacin da gwamnatin Donald Trump ta kaddamar da hare-haren makami mai linzami kan ’yan ta’adda a jihar Sakkwato a ranar Kirsimeti.
Anderson ya ce matakin ya biyo bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Rome ƙarshen shekarar da ta gabata.
“Wannan ya haifar da ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashenmu, ciki har da ƙaramar rundunar Amurka da za ta kawo ƙwarewa na musamman daga Amurka domin ƙarfafa abin da Najeriya ta dade tana yi tsawon shekaru,” in ji Anderson.
Sai dai kwamandan bai bayar da ƙarin bayani ba a kan zuwan nasu, kuma ba a bayyana lokacin da rundunar ta isa Najeriya ba.
A makonnin da suka gabata, mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka, Allison Hooker, ta jagoranci tawagar Amurka mai wakilai daga ma’aikatu takwas zuwa Abuja domin taron haɗin gwiwa da jami’an tsaron Najeriya.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu ne ya jagoranci tawagar Najeriya.
Taron ya biyo bayan sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da gwamnatin Trump ta ayyana a matsayin masu matsala ta musamman (CPC).
Trump ya yi barazanar tura sojoji zuwa Najeriya “da makamai domin kawar da ’yan ta’addan da ke kashe Kiristocinmu.”
A ranar 25 ga Disamba, Amurka ta kaddamar da hare-haren sama kan wuraren da ta ce sansanonin ’yan ta’adda ne guda biyu a dajin Bauni da ke cikin ƙaramar hukumar Tambuwal, Jihar Sokoto.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link